Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Amos 6 - Littafi Mai Tsarki


Halakar Isra'ila

1 Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, Da ku da kuke tsammani kuna zaman lafiya a Samariya, Ku da kuke manyan mutane Na wannan babbar al'umma ta Isra'ila, Waɗanda jama'a suke zuwa a gare su neman taimako!

2 Ku je ku duba a birnin Kalne. Sa'an nan ku zarce zuwa babban birnin Hamat, Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa. Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne? Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi naku?

3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan rana ta masifa, Amma ga shi, goyon bayan hargitsi kuke ta yi, Ta wurin ayyukanku.

4 Taku ta ƙare, ku da kuke kwance kan gadajen hauren giwa, Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayen kujerunku, Ku ci naman maraƙi da na rago.

5 Kukan so ku tsara waƙoƙi kamar yadda Dawuda ya yi, Ku raira su da garayu.

6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi, Ku shafe jiki da mai mafi kyau, Amma ba ku yin makoki saboda lalacewar Isra'ila.

7 Don haka, ku ne na fari da za a sa su yi ƙaura Bukukuwanku da shagulgulanku za su ƙare.

8 Ubangiji kansa ne ya rantse. Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Ba na son girmankai na jama'ar Isra'ila. Ba na son fādodinsu. Zan ba da birnin da dukan abin da yake cikinsa ga abokan gābansu.”

9 Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu.

10 Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?” Sai a amsa, “A'a.” Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”

11 Sa'ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.

12 Dawakai sukan yi sukuwa a duwatsu? Ana huɗan teku da garmar shanu? Duk da haka kuka mai da adalci dafi, Kuka mai da nagarta, mugunta.

13 Kuna fariyar cin garin Lodebar, wato wofi, da yaƙi. Kun ce, “Ƙarfinmu ya isa har mu ci Karnayim, wato ƙaho biyu, da yaƙi.”

14 Ubangiji Allah Mai Runduna kansa, ya amsa ya ce, “Zan aiko da wata al'umma ta yi gāba da ku, ya Isra'ilawa. Za ta matse muku Tun daga mashigin Hamat wajen arewa, Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan