Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Amos 4 - Littafi Mai Tsarki

1 Ku kasa kunne ga wannan, ya ku matan Samariya, Ku da kuka yi ƙiba kamar turkakkun shanu, Ku da kuke wulakanta kasassu, Kuna yi wa matalauta danniya, Kukan umarci mazajenku, Ku ce, “Kawo mini abin sha!”

2 Da yake Ubangiji Mai Tsarki ne Ya riga ya yi alkawari, Ya ce, “Hakika kwanaki za su zo Da za a jawo ku da ƙugiyoyi, Kowannenku zai zama kamar kifi a ƙugiya.

3 Za a kwashe ku, a fitar da ku Ta inda garu ya tsage na mafi kusa duka, a jefar.”


Isra'ila Sun Kāsa Koyo

4 Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila, Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri, Ku yi ta zunubi! Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi! Ku yi ta kawo dabbobi sadaka kowace safiya. A kowace rana ta uku Ku yi ta ba da zaka.

5 Ku miƙa abincinku hadaya ta godiya. Ku yi ta yin fariya da hadayarku ta yardar rai! Gama irin abin da kuke jin daɗin yi ke nan.”

6 Ubangiji ya ce, “Ai, ni ne, na sa a yi yunwa a biranenku. Shi ya sa ba ku da abinci. Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.

7 Na hana wa shuke-shukenku ruwa A lokacin da suka fi bukata. Na sa a yi ruwa a wani birni, A wani birni kuwa na hana, Wata gonar ta sami ruwan sama, Amma wadda ba ta samu ba ta bushe.

8 Ƙishirwa ta sa jama'a su tafke har birane biyu ko uku Suka tafi neman ruwa a birnin da suke maƙwabtaka da shi, A nan ma ba su sami isasshen ruwan sha ba, Duk da haka ba ku komo wurina ba.

9 “Na sa darɓa, da domana Su lalatar da amfanin gonakinku. Fāra kuma ta cinye lambunanku Da gonakin inabinku, da itatuwan ɓaurenku, Da na zaitun ɗinku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.

10 “Na aukar muku da annoba irin wadda na aukar wa Masar. Na karkashe samarinku a wurin yaƙi, Na kwashe dawakanku. Na cika hancinku da ɗoyin sansaninku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.

11 “Na hallakar da waɗansunku Kamar yadda na hallakar da Saduma da Gwamrata. Kamar sanda kuke, wanda aka fizge daga wuta. Duk da haka ba ku komo wurina ba.

12 Saboda haka, jama'ar Isra'ila, Ga abin da zan yi muku, Zan kuwa yi shi duk, Sai ku yi shirin zuwa gaban Ubangiji.”

13 Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan