Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Amos 2 - Littafi Mai Tsarki


Mowab

1 Ubangiji ya ce, “Mutanen Mowab sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun ƙone ƙasusuwan Sarkin Edom Don su yi toka da su.

2 Zan aukar da wuta a ƙasar Mowab, Ta ƙone kagarar Keriyot. Jama'ar Mowab za su mutu a hargitsin yaƙi, Sa'ad da sojoji suke sowa, ana busa ƙahoni.

3 Zan kashe Sarkin Mowab da shugabannin ƙasar.”


Yahuza

4 Ubangiji ya ce, “Mutanen Yahuza sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun raina koyarwata sun ƙi bin umarnaina. Allolinsu na ƙarya waɗanda kakanninsu suka bauta wa, Sun sa su su ratse daga hanya.

5 Saboda haka zan aukar da wuta a kan Yahuza Ta ƙone kagarar Urushalima.”


Allah Ya Hukunta Isra'ila

6 Ubangiji ya ce, “Mutanen Isra'ila sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun sayar da salihai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta Waɗanda bashinsu bai kai ko kuɗin bi-shanu ba.

7 Sun tattake marasa ƙarfi da kāsassu, Suna tunkuɗe matalauta su wuce. Tsofaffi da samari sukan tafi wurin karuwan Haikali. Ta haka suke ɓata sunana mai tsarki.

8 A duk wuraren sujadarsu sukan kwanta A bisa tufafin da suka karɓe jingina. A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sha ruwan inabi Da suka karɓo daga wurin waɗanda suke bi bashi.

9 “Amma ga shi, saboda ku na hallakar da Amoriyawa, Dogayen mutanen nan masu kama da itatuwan al'ul, Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak, Na hallaka su ƙaƙaf.

10 Na fito da ku, wato jama'ata daga Masar. Na bi da ku cikin jeji shekara arba'in, Na kuwa ba ku ƙasar Amoriyawa ta zama taku.

11 Na zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yanku su zama annabawa, Waɗansu kuma daga cikin samarinku su zama keɓaɓɓu. Ko ba haka ba ne, ya ku Isra'ilawa? Ni, Ubangiji, na yi magana.

12 Amma kun sa keɓaɓɓu shan ruwan inabi, Kuka kuma umarci annabawa kada su isar da saƙona.

13 Zan danƙare ku a inda kuke Kamar yadda ake danƙare amalanke da kayan tsaba.

14 Ko masu saurin gudu ma ba za su tsere ba, Ƙarfafa za su zama kumamai, Sojoji kuma ba za su iya ceton kansu ba.

15 'Yan baka ba za su iya ɗagewa ba. Masu saurin gudu ba za su tsira ba. Mahayan dawakai kuma ba za su tsere da rayukansu ba.

16 Ko sojojin da suka fi jaruntaka duka ma, Za su gudu tsirara a ran nan.” Ubangiji ne ya faɗa.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan