M.Sh 2:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Ubangiji Allahnku ya albarkace ku cikin dukan aikin hannuwanku. Ya kiyaye ku cikin tafiyarku a duk fāɗin hamada. Waɗannan shekaru arba’in Ubangiji Allahnku ya kasance tare da ku, ba kuwa kun rasa wani abu ba. See the chapterLittafi Mai Tsarki7 Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’ See the chapter |